PSG ta lashe kofin gasar Faransa na bana

Hakkin mallakar hoto epa
Image caption Karo na shida kenan da PSG ta lashe kofin gasar Faransa

Paris St-Germain ta lashe kofin gasar kwallon kafar Faransa, duk da saura watanni biyu a kammala gasar bana.

PSG ta samu damar daukar kofin ne kuma a karo na hudu a jere kuma na shida jumulla, bayan da ta doke Troyes da ci 9-0 a wasan mako na 30 wanda suka fafata a ranar Lahadi.

Haka kuma a gasar ta Faransa ta bana sau daya aka doke PSG, wato a wasan da Lyon ta ci ta 2-1 a watan Fabrairu,

PSG ta kuma ci kwallaye 77 aka zura mata 15 a raga, inda ta lashe wasanni 24 daga 30 da ta buga, kuma Ibrahimovic ne ya fi ci mata kwallaye wanda ya ci 31 a wasanni 25 da ya buga mata.