Wartford ta fitar da Arsenal daga kofin FA

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Arsenal tana mataki na uku a kan teburin Premier

Watford ta doke Arsenal da ci 2-1 a gasar cin kofin FA da suka kara a Emirates a ranar Lahadi, ta kuma cire Arsenal wadda ta ke rike da kofin bara.

Odion Ighalo ne ya fara cin Arsenal bayan da aka dawo daga hutun rabin lokaci, kuma Adlene Guedioura ya kara kwallo ta biyu a ragar ta Arsenal.

Daf da aka kusa tashi daga wasan ne Arsenal ta zare kwallo daya ta hannun Danny Welbeck bayan da Ozil ya ba shi tamaula da dunduniya.

Wannan shi ne karo na uku da aka ci Arsenal a Emirates a jere, inda Swansea da Barcelona da Watford suka doke ta, kuma rabon da a yi mata hakan tun 2006 a filin Highbury.