FA ta tuhumi Costa da halin rashin da'a

Hakkin mallakar hoto bbc
Image caption FA ta bai wa Costa zuwa ranar Alhamis domin ya kare kansa

Hukumar kwallon kafa ta Ingila, ta tuhumi dan wasan Chelsea, Diego Costa da nuna halin rashin da'a a karawar da suka yi da Everton a ranar Asabar.

An kori Costa daga fili ne saura minti hudu a tashi daga wasan da Everton ta doke Chelsea 2-0 a gasar cin kofin kalubale karawar daf da na kusa da karshe da suka yi a Goodison Park.

An kuma nuna wani hoton bidiyo da yake nuna Costa ya ciji Gareth Baryy, koda yake dukkan 'yan wasan biyu sun karyata aikata laifi a wasan.

Saboda haka hukumar kwallon kafar ta tuhumi dan wasan ne bisa halin da ya nuna a lokacin da aka bashi jan katin da kuma kin fita daga fili da wuri.

Hukumar ta bai wa Costa zuwa ranar Alhamis da maraice domin ya kare kansa daga tuhumar da take yi masa.