Everton za ta kara da United ko West Ham

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption West Ham tana mataki na 5 a kan teburin Premier, yayin da United ke matsayi na 6

Everton za ta fafata da Manchester United ko kuma West Ham a gasar cin kofin FA wasan daf da na karshe, sai Crystal Palace ta karbi bakuncin Watford.

Kungiyoyin za su kara ne tsakanin 23 ga wata da kuma 24 ga watan Afirilu a filin wasa na Wembley.

Manchester United za ta buga wasa na biyu da West Ham a Upton Park, bayan da suka tashi 1-1 a ranar Lahadi a Old Trafford a wasan daf da na kusa da karshe.

Hukumar kwallon kafa ta Ingila za ta sanar da ranar da United za ta ziyarci Upton Park ne bayan an kammala karawa tsakanin Manchester United da Liverpool a gasar Europa League.