Uefa ba za ta hukunta United da Fellaini ba

Hakkin mallakar hoto rex features
Image caption Ranar Alhamis ce Liverpool za ta ziyarci Old Trafford

Hukumar kwallon kafa ta Turai, UEFA, ba za ta ladabtar da Manchetser United ba saboda wakar batanci da magoya bayanta suka rera dangane da bala'in da ya faru a filin wasan Liverpool, wato Hillsborough.

Magoyan bayan Manchester United din sun rera wakar ne yayin wasan Gasar Europa da kungiyoyin suka buga, lokacin da United ta sha kashi a hannun Liverpool.

Shi ma dan wasan United Marouane Fellaini ya tsallake hukuncin ladabtarwa saboda zargin yi wa Emre Can kulli a karshe-karshen wasan.

UEFA ta yanke shawarar ba za ta dauki mataki ba ne saboda jami'an da suka yi alkalancin wasan ba su rubuta lamuran biyu ba a rahotonsu na wasan.

Liverpool ce ta lashe zagayen farko na wasan na matakin 'yan-16 da ci biyu a Anfield. Ranar Alhamis ne kuma za a buga zagaye na biyu na wasan.

Jami'ai na shirin kasa kunne sosai don tantance wakokin da za a rera a Old Trafford.