UEFA: City ta kai wasan daf da na kusa da karshe

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption A karon farko City ta kai wasan daf da na kusa da karshe a gasar zakarun Turai

Manchester City ta kai wasan daf da na kusa da karshe a karon farko a gasar cin kofin Zakarun Turai.

City ta samu kai wa wasan gaba ne a gasar duk da tashi wasa canjaras babu ci da ta buga da Dynamo Kiev a Ettihad, a wasan farko da suka yi a Ukraine City ce ta samu nasara da ci 3-1.

Manchester City ta fara buga gasar cin kofin zakarun Turai na Champions League a kakar wasan 2011/12, kuma ba ta taba kai wa wannan matakin ba a gasar.

City tana matsayi na hudu a kan teburin Premier da maki 51, kuma a karshen kakar bana ne Pep Guardiola zai maye gurbin Manual Pellegrini a Ettihad