Gareth Bale ba zai buga wa Wales wasa ba

Image caption Wales za ta buga wasan sada zumunta da Ireland ta Arewa da kuma Ukraine

Gareth Bale ba zai buga wa Wales wasan sada zumunta da za ta yi da Ukraine ba, sakamakon haihuwa da matarsa za ta yi karo na biyu.

A wannan lokacin ne ake sa ran matar Bale, Emma Rhys-Jones, za ta haihu a wani asibiti a Spaniya.

Wales za ta buga wasan sada zumunta da Ireland ta Arewa ranar 24 ga watan Maris, sannan ta ziyarci Ukraine kwanaki hudu tsakani.

Wales za ta yi wasannin sada zumunta ne domin tunkarar wasannin gasar cin kofin nahiyar Turai da Faransa za ta karbi bakunci a bana.

Haka shi ma Aaron Ramsey na Arsenal da James Collins na West Ham da kuma Dave Edwards na Wolves ba za su buga wasannin ba, sakamakon jinya da suke yi.