Kompany zai yi jinyar wata daya

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Kompany ya shiga tsaka mai wuya

Manchester City za ta yi rashin kyaftin din Vincent Kompany na tsawon wata guda saboda raunin da ya ji a wasansu da Dynamo Kiev.

Dan kasar Belgium din mai shekaru 29, a kakar wasa ta bana ya nata fama da laulayi.

"Vincent ya kara jin rauni irin wanda ya dade yana fama da shi," in ji Pellegrini.

Ana saran a ranar Laraba ko Alhamis za a dauki hoton kafar Kompany.

Kompany ba zai buga wasansu na hammaya ba da Manchester United, kuma watakila ba zai buga wasan farko a zagaye na gaba ba a gasar zakarun Turai a farkon watan Afrilu.