Babu korafi kan gasar Firimiyar Nigeria - Dikko

Image caption A karshen makonnan za a ci gaba da wasannin mako na bakwai a gasar Firimiyar Nigeria

A karshen makon nan ne za a shiga wasannin mako na bakwai a gasar Premier Nigeria.

Shugaban hukumar gudanar da gasar Shehu Dikko, ya ce har yanzu ba su sami korafi ba dangane da yadda aka fara yin wasannin.

Dikko ya ce a gasar bara, tun a wasannin mako na uku suka fara hukunta alkalan wasan gasar da kungiyoyi kan laifukan karya dokar hukumar.

Shugaban ya kuma ce abin alfahari ne a wasannin bana da kungiyoyi ke samun nasara a wasannin waje, a kuma tashi wasa ba tare da matsala ba.

Bayan da aka buga wasannin mako na shida a gasar an ci wasanni biyar a waje sannan aka yi kunnen doki a fafatawa 11.