Zan dawo kan ganiyata - Shagon Mada

Hakkin mallakar hoto bbc
Image caption Kamalu Tanimu da aka fi sani da suna Shagon Mada dan wasan damben gargajiya daga Kudu

Shagon Mada dan wasan damben gargajiya mai wakiltar Kudawa ya ce zai dawo kan ganiyarsa a dambe.

Dan damben mai cikakken suna Kamalu Tanimu ya ce a yanzu a kwai shirye shiryen da yake yi da kuma kariya domin bunkasa wasan da yake yi.

Shagon Mada ya kuma ce damben gargajiya ya yi masa rana ya kuma samu alhairai da yawa, sakamakon hazakar da yake nunawa.

Ya kara da cewa shi dan kasuwa ne ya kuma iya dinki da sauran kasuwanci, idan ya yi ritaya daga wasan yana da sana'oin da zai yi

Shagon Mada ya kuma gode wa magoya bayansa da suke kara masa kwarin gwiwa a wasannin da yake yi, ya ce ba zai ba su kunya ba.