Zan zauna a Leicester har ritaya - Ranieri

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Kociyan Leicester, Claudio Raneiri

Kociyan Leicester, Claudio Ranieri ya ce yana son cigaba da zama a kulob din har lokacin ritaya.

Ya ce "ina son cigaba da zama a nan. Babu wata kungiyar da za ta na sauya tunanina. Ina jin dadin kasancewa da Leicester."

a watan Yuli ne dai tsaohon kociyan na Chelsea ya koma Leicester a kan kwantaragin shekara uku.

Leicester dai ita ce ta daya a saman teburin gasar Premier kuma akwai tazarar maki biyar tsakaninta da mai biye mata wato Tottenham.