Euro 2016: Ingila ta kira Drinkwater

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Dan wasan Leicester, Danny Drinkwater

An sanya sunan dan wasan tsakiya na Leicester, Danny Drinkwater a jerin sunayen wadanda za su takawa Ingila leda a wasanni gabanin gasar Euro 2016.

Ingilar dai za ta kara da Jamus ranar Asabar 26 ga Maris sannan kuma za ta karbi bakuncin Netherlands, ranar Talata 29 ga Maris.

Wannan dai shi ne karon farko da dan wasan mai shekara 26 ya samu gayyata daga babbar kungiyar wasa ta kasa.

Dan wasan Tottenham, Danny Rose da dan wasan Liverpool, Daniel Sturridge suna cikin 'yan wasan na Ingila.

Sai dai kuma Wayne Rooney ba ya cikin kungiyar saboda raunin da ya ji a gwiwa.