FIFA: An fara binciken Jerome Valcke

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ana tuhumar Jerome Valcke da hannu a almubazzaranci.

Masu binciken laifuka a Switszerland sun fara tuhumar tsohon babban sakataren hukumar wasan kwallon kafa ta FIFA.

An dai sanya Valcke ya tafi hutu sannan kuma aka sallame shi daga aikin nasa a watan Satumba.

An zarge shi ne da hannu a badakala da dama.

Sai dai kuma ba a tsare shi ba amma ya fuskanci tambayoyi daga masu bincike kan laifukan almubazzaranci.