Messi, Suarez da Neymar jarumai ne - Wenger

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Messi da Neymar da Suarez.

Kociyan Arsenal, Arsene Wenger ya ce 'yan wasan Barcelona 'yan uku wato Messi da Neymar da Suarez sun maida rayuwarsu ta zama fagen da za a iya nazarta.

A ranar Laraba ne dai Barcelona ta yi waje da Arsenal daga gasar zakarun turai, a wasan da suka tashi 3-1.

Kuma kowanne daga cikin 'yan wasan uku ya jefa kwallo daya a ragar ta Arsenal.

A don haka ne Wenger ya bayyana su da jarumai.

An dai yi kiyasin darajar 'yan wasan a kasuwar musayar 'yan wasa a kan kudi £232.5m.