Liverpool ta sayi 'yar Asisat Oshoala

Asisat ce ta lashe kyauta ta farko ta gwarzuwar 'yar kwallon kafa ta BBC
Bayanan hoto,

Asisat ce ta lashe kyauta ta farko ta gwarzuwar 'yar kwallon kafa ta BBC

Kungiyar kwallon kafa ta mata ta Arsenal ta sayi 'yar wasan gaba ta Najeriya, Asisat Oshoala daga Liverpool kan farashin da ba a bayyana ba.

Oshoala ta ci wa Liverpool kwallaye uku a wasanni 12 a kakar wasanni ta bara, bayan da ta shiga kungiyar a watan Janairun 2015.

'Yar wasan mai shekaru 21 ta lashe kyauta ta farko ta gwarzuwar 'yar kwallon kafa ta BBC a shekarar da ta gabata.

Kociyan kungiyar Pedro Losa, ya ce, "Asisat kwararriyar 'yar wasa ce kuma za taka rawa sosai a kungiyarmu."

"Tana da hanzari ta kuma iya taka leda, sannan ta nuna cewa za ta ci kwallaye da yawa, don haka abu ne mai kyau da ta yanke shawarar kasancewa tare da mu," a cewar Mista Losa.

Sai dai har zuwa yanzu ba a sanar da tsawon lokacin da kwantiragin nata zai kai ba.