Alaba ya sabunta kwantaraginsa a Bayern

Bayern Munich, David Alaba Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Alaba na haskakawa a Bayern

Dan kwallon Bayern Munich, David Alaba ya sabunta kwangilarsa zuwa karin shekaru uku domin ci gaba da murza leda har zuwa shekara ta 2021.

Dan wasan Austria mai shekaru 23, ana alakanta shi da koma wa Manchester City, tare da Pep Guardiola wanda zai bar Bayern.

Alaba ya lashe kofunan gasar Bundesliga hudu da kuma na zakarun Turai tun lokacin da ya soma wasa a Bayern a shekara ta 2010.

"Zai ci gaba da zama daya daga cikin manyan 'yan wasanmu," in ji shugaban Bayern,Karl-Heinz Rummenigge.

Alaba ya buga wasanni 22 daga cikin 26 a kakar wasa ta bana a gasar ta Jamus.