Chelsea da West Ham sun tashi 2-2

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Chelsea tana nan a matakinta na 10 a kan teburin Premier

Chelsea ta tashi wasa 2-2 da West Ham a gasar Premier wasan mako na 31 da suka kara a Stamford Bridge ranar Asabar.

West Ham ce ta fara cin kwallo ta hannun Manuel Lanzini a kwallon da ya buga tun daga yadi na 25 a minti na 17 da fara wasan.

Daf da za a ta fi hutun rabin lokaci ne Fabregas ya farkewa Chelsea kwallon da aka zura mata.

Andy Carroll ne ya ci wa West Ham kwallo ta biyu, kuma Fabregas ya kara ci wa Chelsea ta biyun shi kuma a bugun fenariti.

Chelsea wadda har yanzu ba a doke ta a gasar Premier a karkashin kociyan rikon kwarya Guus Hiddink, tana nan a matakinta na 10 a kan teburi.