Leicester ta bayar da tazarar maki takwas

Image caption Leicester City ta ci gaba da zama a mataki na daya a kan teburin Premier

Leicester City ta doke Crystal Palace da ci daya mai ban haushi a gasar Premier wasan mako na 31 da suka yi a ranar Asabar.

Leicester ta ci kwallonta ne a Sehust Park ta hannun Riyad Mahrez saura minti 11 ya rage a je hutun rabin lokaci.

Da wannan sakamakon da Leicester wadda ta buga wasanni 31 ta bai wa Tottenham wadda ke biye da ita bayan wasanni 30 da tazarar maki biyu.

Crystal Palace wadda rabonda ta samu nasara a gasar Premier tun a cikin watan Disamba, ta kai wasan daf da karshe a gasar cin kofin kalubalen Ingila.