Dan Sama'ila da Dan Aminu sun yi canjaras

Image caption Sau biyu suka dambata babu kisa aka raba fafatawar

Dan Aminu Shagon Langa-Langa daga Arewa da Dan Sama'ila Shagon Alabo daga Kudu sun tashi wasa babu wanda ya je kasa a wasan damben gargajiya da suka fafata a ranar Lahadi.

Damben da suka yi turmi biyu alkalin wasa Shagon Amadi ya raba su, daya ne daga cikin fafatawa takwas da aka yi a gidan damben Ali Zuma dake Dei-Dei a Abuja Nigeria.

Wasannin damben gargajiya da aka yi a ranar Lahadi sun ci 'yan kallo, domin babu karawar da aka yi kisa a ranar.

Ga wasanni takwas din da aka fafata a damben Lahadi babu kisa:
  1. Dan Jere daga Arewa da Shagon Autan Faya daga Kudu
  2. Jirgin Taye daga Kudu da Shagon Shagon Alhazai daga Arewa
  3. Shagon Inda daga Arewa da Kurarin Kwarkwada daga Kudu
  4. Nuran Dogon Sani daga Arewa da Bahagon Dan Kanawa daga Kudu
  5. Abban Na Bacirawa daga Arewa da Bahagon Fandam daga Kudu
  6. Dan Sama'ila Shagon Alabo daga Kudu da Aminu Langa-Langa daga Arewa
  7. Sarka daga Kudu da Autan Na Dutsen Mari daga Arewa
  8. Garkuwan Shagon Alabo daga Kudu da Shagon Musan Kaduna daga Arewa