Newcastle da Sunderland sun tashi wasa 1-1

Hakkin mallakar hoto Rex Features
Image caption Newcastle United da Sunderland sun tashi 1-1 a karawar hamayya

Newcastle United da Sunderland sun tashi wasa canjaras babu ci a wasan cin kofin Premier da suka fafata a St James Park ranar Lahadi.

Sunderland ce ta fara cin kwallo ta hannu Jermain Defoe daf da za a je hutun rabin lokaci.

Newcastle United ta farke kwallo ne ta hannun Aleksandar Mitrovic saura minti takwas a tashi daga karawar.

Da wannan sakamakon da suka tashi Sunderland tana matsayi na 18 a kan teburin Premier da maki 26.

Ita kuwa Newcastle United tana mataki na 19 a kan teburin da maki 25.