El-Kanemi ta samu nasara a kan Ifeanyiubah

Hakkin mallakar hoto HeartlandFC twitter
Image caption Sakamakon wasannin mako na bakwai a gasar Firimiyar Nigeria

El-Kanemi Warriors ta doke Ifeanyiubah da ci 2-1 a gasar Firimiyar Nigeria wasan mako na bakwai da suka fafata a ranar Lahadi.

Okereke Maduabuchi ne ya fara ci wa Ifeanyiubah kwallo a minti na takwas da fara tamaula, kuma daf da za a je hutu El-Kanemi ta farke kwallon ta hannun Ibrahim Mustapha.

El-Kanemin ta kara cin ta biyu ne saura minti 15 a tashi daga karawar ta hannun Agoha Otakho.

Ga sakamakon sauran wasannin mako na bakwai da aka yi:
  • Heartland 1-0 MFM FC
  • Plateau Utd 2-1 Lobi
  • Rangers 3-0 Akwa Utd
  • Wikki 2-1 Tornadoes
  • Ikorodu Utd 1-2 Giwa FC
  • Shooting Stars 1-0 Rivers Utd