Za a buga wasannin Premier a Afirka

Image caption Arsenal ce ta lashe wasannin da aka yi a nahiyar Asia a 2003

Babban jam'in gasar Premier Ingila, Richard Scudamore, ya ce nahiyar Afirka za ta iya karbar bakuncin wasannin sada zumuntar kungiyoyin Premier.

A shekarar 2003 nahiyar Asia ta karbi bakuncin kungiyoyin Premier hudu da suka fafata a wasannin share fagen tunkarar gasar ta Ingila.

Scudamore ya ce nahiyar Afirka ma ta cancanci ta karbi bakuncin wasannin share fage na kungiyoyin gasar ta Premier.

Ya kuma ce sun samu karbuwa a nahiyar Asia, ya kamata a yi a Afirka da kuma Amurka.

Scudamore ya fadi hakan ne a wani shiri na kai tsaye da mahukuntan gasar suka shirya a Afirka ta Kudu ranar 19 da kuma 20 ga watan Maris.