Bale ya dara Lineker cin kwallaye a Spaniya

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Real Madrid tana mataki na uku a kan teburin La Liga

Gareth Bale ya kafa tarihin dan wasan Birtaniya da ya fi cin kwallaye a gasar La Liga, wanda hakan ya sa ya haura Garry Lineka.

Bale ya ci kwallo ne a wasan da Real Madrid ta dode Sevilla da ci 4-0 a gasar La Liga wasan mako na 30 da suka kara a ranar Lahadi.

Kwallon da Bale ya ci ita ce ta 43 jumulla daga wasanni 76 da ya buga a La Liga, inda ya haura Gary Lineker wanda ya yi wa Barcelona wasanni 103 ya ci kwallaye 42 a baya.

Nasarar da Real Madrid ta samu a wasan ya sa tana nan a matakinta na uku da maki 66, da tazarar maki 10 tsakaninta da Barcelona mai matsayi ta daya a teburi.