Guardiola zai koma Man City komai runtsi

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Manchester City tana mataki na hudu a kan teburin Premier

Pep Guardiola zai koma horar da tamaula a Manchester City a badi, koda kungiyar bata samu gurbin shiga gasar cin kofin zakarun Turai ba.

A bana ne Guardiola, wanda ke jan ragamar Bayern Munich, ya saka hannu kan yarjejeniyar kwantiragin horar da City tamaula na tsawon shekara uku.

Kociyan zai maye gurbin Manuel Pellegrini, ya kuma karyata cewar ya saka hannu kan yarjejeniyar kin komawa City idan ba su kare a hudun farko ba a gasar Premier.

Rashin nasara da City ta yi a hannaun Manchester United ya sa tana mataki na hudu a kan teburi da zarar maki daya tsakaninta da West Ham da kuma United.

Guardiola tsohon kociyan Barcelona bai taba jagorantar kungiya ba a gasar Europa League.