Fifa na binciken Beckenbauer kan badakala

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Jamus ce ta samu damar karbar bakuncin kofin duniya kan Afirka ta Kudu a 2006

Fifa, ta ce tana binciken Franz Beckenbauer, kan rawar da ya taka a karbar bakuncin gasar cin kofin duniya a 2006 da aka yi a Jamus.

Kwamitin da'a na hukumar ya fara binciken tsohon kyaftin din Jamus din ne, bayan ya duba wani rahoto da hukumar kwallon kafa ta Jamus ta fitar, kan gasar kofin duniyar.

Wani rahoto da jaridar Jamus mai suna Der Spiegel ta fitar a bara, ta ce ana zargin biyan sama da fam miliyan hudu domin sayen kuri'u, kan a zabi Jamus, hukumar kwallon kafa ta Jamus ta karyata zargin.

A watan Oktoba, Beckenbauer, mai shekara 70 ya ce ya yi kuskure a lokacin zabar kasar da za ta karbi bakuncin wasannin duniya, ya kuma dauki alhakin kuskuren da ya yi.

Jamus ce ta samu nasarar karbar bakuncin wasannin cin kofin duniyar da aka yi a watan Yulin 2000, Jamus ta samu kuri'u 12, Afirka ta Kudu 11.

Fifa za ta binciki Beckenbauer da Zwanziger da Schmidt da kuma Hans kan zargin bayar da cin hancin zaben Jamus, za kuma ta binciki Niersbach da Sandrock kan kin bayyana karya ka'idojin hukumar.