U-17: Nigeria za ta ziyarci Afirka ta Kudu

Hakkin mallakar hoto The NFF Twitter
Image caption Nigeria 6-0 ta doke Afirka ta Kudu a wasan farko da suka yi a Abuja

Tawagar kwallon kafa ta mata ta Nigeria za ta ziyarci Afirka ta Kudu, domin karawa a wasa na biyu na neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya.

A karawar farko da aka buga a Abuja, Nigeria ce ta samu nasara da ci 6-0 a wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya ta mata 'yan kasa da shekara 17.

Nigeria ta halarci gasar cin kofin duniya ta matasa 'yan kasa da shekara 17 ta mata tun lokacin da aka kirkiro gasar a shekarar 2008 a New Zealand.

Za a buga wasan cin kofin duniyar ne ta matasa a Jordan daga 30 ga watan Satumba zuwa 31 ga watan Oktoban shekarar nan.