Belgium za ta kara da Portugal a Leiria

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mutane 30 ne suka mutu a harin bam din da aka kai filin jirgin sama na Brussels

Tawagar kwallon kafa ta Belgium za ta ziyarci Portugal domin buga wasan sada zumunta a Leiria.

Tun farko an tsara buga karawar ce a Belgium, amma bisa kai harin ta'addanci da aka kashe mutane 30 a Brussels ya sa aka dage wasan.

Portugal ce ta yi tayin karbar bakuncin wasan bayan da Belgium ta dage fafatawar sakamakon dalilin tsaro.

Portugal din za ta kara da Belgium ne a ranar Talata, kuma tawagar ta Belgium za ta yi atisaye a filin wasa na King Baudouin a ranar Laraba.

Wannan ne karo na biyu da ake dage wasannin da Belgium ta shirya sakamakon rashin tsaro.