MFM da Kano Pillars sun tashi wasa 1-1

Hakkin mallakar hoto HeartlandFC twitter
Image caption MFM da Kano Pillars sun tashi wasa kunnen doki 1-1

Kano Pillars ta samu maki daya a karawar da ta tashi kunnen doki da MFM a gasar Firimiyar Nigeria wasan mako na takwas da suka kara ranar Laraba.

MFM ce ta fara cin kwallo a minti na 28 da fara tamaula ta hannun Stanley Okorom.

Pillars ta farke kwallon da aka zura mata ta hannun Rabiu Ali a bugun fenariti, bayan da Monsuru ya rike Aggreh a da'ira ta 18 bayan an dawo daga hutu.

Da wannan sakamakon Kano Pillars ta hada maki 12 a wasanni bakwai da ta yi, yayin da MFM keda maki 14 a karawa takwas da ta buga a gasar.