IfeanyiUbah ta doke Heartland 1-0

Hakkin mallakar hoto NPFL Twitter
Image caption Lobi Stars ce ta doke Enugu Rangers da ci 3-1

IfenyiUbah ta samu nasara a kan Heartland da ci daya mai ban haushi a gasar cin kofin Firimiyar Nigeria wasan mako na takwas da suka yi ranar Laraba.

William Da Silva ne ya ci kwallon da ta bai wa IfeanyiUbah maki uku a karawar da suka yi.

Sauran sakamakon wasannin mako na takwas da aka buga, Lobi Stars ta doke Enugu Rangers da ci 3-1, sai Giwa da El-Kanemi da suka tashi 1-1.

Wasan Abia Warriors da Wikki da na Rivers United da Sunshine Stars da kuma na Akwa United da Warri Wolves tashi suka yi babu ci.

Sai da dare ne MFM za ta yi gumurzu da Kano Pillars a jihar Legas, ranar Alhamis a kara tsakanin Enyimba da Plateau United da karawa tsakanin Nasarawa United da Ikorodu United.

Sakamakon wasannin mako na takwasa da aka yi:
  • Lobi Stars 3-1 Rangers
  • Tornadoes 2-1 Shooting Stars
  • FC Ifeanyiubah 1-0 Heartland
  • Giwa FC 1-1 El-Kanemi
  • Abia Warriors 0-0 Wikki
  • Rivers United 0-0 Sunshine Stars
  • Akwa United 0-0 Warri Wolves