Watakila Sterling ya gama buga wasannin bana

Hakkin mallakar hoto Reax Features
Image caption Manchester City tana mataki na hudu a kan teburin Premier da maki 51

Dan wasan Manchester City, Raheem Sterling, zai yi jinyar makonni shida zuwa takwas, kuma hakan na nufin ya gama buga wasannin bana.

Sterling mai shekara 21, ya ji rauni ne a wasan da Manchester City ta yi rashin nasara a hannun Manchester United 1-0 a gasar Premier a ranar Lahadi.

Yin jinyar makonni takwas na nufin Sterling, zai dawo da taka leda a satin da za a buga wasannin karshe na gasar Premier ranar 15 ga watan Mayu.

Yayin da ake sa ran buga wasan karshe a gasar cin kofin zakaraun Turai ranar 28 ga watan Mayu.

Ingila za ta nazarci murmurewar dan wasan domin hakikance idan Sterling zai iya wakiltarta a gasar cin kofin nahiyar Turai da Faransa za ta karbi bakunci a bana.

A ranar 12 ga watan Mayu ake sa ran kociyan tawagar kwallon kafar Ingila, Roy Hodgson, zai fitar da sunayen 'yan wasa 23 da za su wakilceta a gasar Turai.