Morocco ta hana shiga filin wasa da makamai

Image caption Mutane uku ne suka mutu, 54 suka samu raunuka

Jami'ai a Moroko sun soke duk wasu ayyukan gungun magoya bayan kungiyoyin kwallon kafar kasar, sakamakon yamutsi da aka samu a Casablanca ranar Asabar.

Kimanin mutane uku ne suka mutu, 54 kuma suka samu rauni a karawar da Raja Casablanca ta doke Chabab Rif Al Hoceima da ci 2-1 a ranar Asabar.

Hukumar kwallon kafar kasar ta amince da magoya bayan Raja Casablanca su kalli wasannin kungiyar da za ta buga a gasar a gaba.

Sai dai kuma an hana shiga filin wasa da duk wasu abubuwa masu tartsatsin wuta da kuma kyallaye masu dauke da sakon nuna goyon bayan kungiya.