Arsenal na bukatar Arsene Wenger

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Wenger ya fara horar da Arsenal a cikin shekarar 1996

Wanda ya fi yawan hannun jari a Arsenal, Alisher Usmanov, ya ce kulob din na bukatar Arsene Wenger, kuma kociyan ne ya kamata ya fadi ranar da zai bar Gunners din dan radin kansa.

Usmanov ya kuma ce ya kamata a saka Wenger cikin tsarin wanda zai fayyace yadda Arsenal za ta ci gaba da samun nasarori ko da ya bar kungiyar.

Ya kuma ce Arsenal ta kasa lashe manyan kofuna ne sakamakon rashin sa'a a shekaru da dama, kuma kungiyar ba za ta dauki kofin Premier na bana ba.

An fitar da Arsenal daga kofin zakarun Turai a wasan zagaye na biyu kuma karo na shida kenan da ake cire ta a wannan matakin a gasar, da kuma doke ta da Watford ta yi a kofin FA.

Arsenal ta na mataki na uku a kan teburin Premier da tazarar maki 11 tsakaninta da Leicester wadda ke matsayi na daya, kuma rabon da ta dauki kofin tun a shekarar 2004.

Wenger wanda ya fara jagorantar Arsenal tun daga shekarar 1996 na shan suka daga wajen magoya bayan kungiyar cewa ya ajiye aikin da ya ke yi a yanzu.