U-17 Mata: Nigeria ta doke Afirka ta Kudu

Hakkin mallakar hoto The NFF Twitter
Image caption Jumulla Nigeria ta doke Afirka ta Kudu da ci 7-0 a wasa biyu da suka fafata

Tawagar kwallon kafa ta mata ta matasa 'yan kasa da shekara 17 ta Nigeria ta doke ta Afirka ta Kudu da ci 1-0 a wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya ta matasa.

Nigeria ta ci kwallonta ne ta hannun Rasheedat Ajibade saura minti 17 a tafi hutun rabin lokaci a karawar da suka yi a filin wasa na Makhulong ranar Asabar.

A wasan farko da suka kara a Abuja, Nigeria ce ta doke Afirka ta Kudu da ci 6-0, jumulla Flamingoes ta ci Bantwana 7-0.

Da kuma wannan nasarar da Nigeria ta samu ya sa ta samu gurbin shiga gasar cin kofin duniya ta matasa 'yan kasa da shekara 17 da za a yi a Jordan.

Kasashe uku ne ke wakiltar Afirka a wasan gasar cin kofin duniya ta matasa 'yan kasa da shekara 17.