Pillars za ta karbi bakuncin Ifeanyi Ubah

Hakkin mallakar hoto HeartlandFC twitter
Image caption Ranar Lahadi za a ci gaba da wasannin mako na tara a gasar Firimiyar Nigeria

Kano Pillars za ta karbi bakuncin Ifeanyi Ubah a gasar cin kofin Firimiyar Nigeria wasan mako na tara da za su yi a ranar Lahadi a jihar Kano.

Pillars wadda ta buga wasanni bakwai a gasar tana mataki na biyar a kan teburi da 12, ita ma Ifeanyi Ubah wasanni bakwai ta yi, tana kuma da maki 13 a matsayi na hudu.

Wasu daga cikin wasannin da za a buga Rangers da Enyimba za su kara a Enugu a wasan hamayya da fafata tsakanin Ikorodu United da Rivers United.

El-Kanemi Warriors za ta karbi bakuncin Nasarawa United ne, da karawar da Shooting Stars za ta ziyarci Sunshine Stars a Akure.

Ga jerin wasannin mako na tara a gasar Firimiyar Nigeria:
  • Sunshine Stars vs Shooting Stars
  • Ikorodu United vs Rivers United
  • El-Kanemi Warriors vs Nasarawa United
  • Heartland vs Giwa
  • Plateau United vs MFM
  • Rangers Int'l vs Enyimba International
  • Warri Wolves vs Lobi Stars
  • Wikki Tourists vs Akwa United
  • Abia Warriors vs Niger Tornadoes