Milner zai yi kyaftin din Ingila a karawarta da Netherlands

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Roy Hodgson zai yi sauye-sauye a kungiyar.
Dan wasan tsakiya na Liverpool James Milner ne zai zama kyaftin Ingila a wasan sa da zumunta da za su yi da Netherlands a ranar Talata.

Wannan ne zai zama karo na 30 da dan wasan mai shekara 30 zai jagorancin kasarsa.

Ana sa ran koci Roy Hodgson zai yi sauye-sauye da dama sakamakon ci 3-2 da suka yi a Jmasu, inda Fraser Forster zai maye gurbin Jack Butland da ya ji rauni.

Ita kuwa tawagar kwallon Netherlands ta kara Michel Vorm da Marco van Ginkel cikin 'yan wasan da za su fafata.

Kungiyar wasa ta Netehrlands dai ba ta samu damar hayewa wasan cancanta na gasar Turai na 2016 ba da aka yi a Faransa.