An yi waje da Murry daga gasar Miami Open

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Dimitrov ne ya fitar da Murray daga gasar ta Miami Open

Dan wasan kwallon tennis din Birtaniya, Andy Murray, ya yi ban kwana da gasar Miami Open, bayan da ya sha kashi a hannun Grigor Dimitrov.

Murry mai shekara 28, ya yi rashin nasara ne a wasan zagaye na uku a gasar da ci 6-7 (1-7) 6-4 6-3.

Da wannan sakamakon, Dimitrov dan kasar Bulgeria ya lashe fafatawa biyar zai kuma kara a wasan zagaye na gaba.

Tunda farko, Johanna Konta ta zama 'yar wasan kwallon tennis 'yar Birtaniya ta farko da ta kai wasan daf da na kusa da karshe a gasar, inda Heather Watson kuwa ta yi rashin nasara a hannun Simona Halep.