AFCON 2017: Guinea ta doke Malawi 2-1

Image caption Guinea ta koma mataki na biyu a kan rukuni biye da Zimbabwe

Malawi ta yi rashin nasara a hannun Guinea da ci 2-1 a wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka da suka fafata a ranar Talata.

Malawi ce ta fara cin kwallo ta hannun Chiukepo Msowoya, a minti na 32 da fara tamaula, daf da za a je hutu Guinea ta zare kwallon ta hannun Mohamed Yattara.

Bayan da aka dawo daga hutu ne Guinea ta ci kwallo ta biyu ta hannun Idrissa Sylla, wanda hakan ne ya ba ta damar samun maki uku a wasan.

Da wannan sakamakon da Guinea ta samu ya sa tana mataki na biyu da maki biyar a kan teburi da tazarar maki uku tsakaninta da Zimbabwe wadda ke mataki na daya da maki takwas.