Butland ba zai buga gasar kofin Turai ba

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Jack Butland shi ne mai tsaron ragar Stoke City mai buga gasar Premier

Mai tsaron ragar Tawagar Ingila, Jack Butland, ba zai buga gasar cin kofin nahiyar Turai ba, sakamakon karyewa da ya yi a wasan sada zumunta da Jamus, ranar Asabar.

A ranar Talata ne likitoci za su yi wa Butland, mai shekaru 23, tiyata, wanda har yanzu ba a sanar da kwanakin da zai yi jinya ba.

Bayan da Butland ya ji rauni ne za a fitar da shi daga fili sai kawai ya barke da kuka, hakan ya sa kociyan tawagar Ingila, Roy Hodgson ya ce raunin abin takaici ne.

Mai tsaron ragar wanda ke murza leda a Stoke City da ke buga gasar Premier, ya buga wa tawagar Ingila wasanni hudu kacal.