Messi ya kusa kamo Batistuta a cin kwallaye

Image caption Lionel Messi ya ci wa Argentina kwallaye 50 a raga

Lionel Messi ya kusa ya kamo Gabriel Batistuta, a matsayin dan wasan da yafi ci wa tawagar Argentina kwallaye.

Messi dan wasan Barcelona, ya ci wa Argentina kwallo na 50 a karawar da suka doke Bolivia 2-0, a wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya da suka yi ranar Talata.

Tsohon dan wasan Fiorentina da kuma Roma, Gabriel Batistuta, ya ci wa tawagar kwallon kafa ta Argentina kwallaye 56 a matsayin wanda yake kan gaba.

Messi wanda ya lashe kyautar dan wasan tamaula da ya fi yin fice a duniya karo biyar, ya ci kwallaye 449 a dukkan wasannin da ya yi.