Kwantan wasannin Firimiyar Nigeria

Hakkin mallakar hoto HeartlandFC twitter
Image caption An buga wasanni tara a gasar ta Firimiyar Nigeria

Ifeanyiubah za ta karbi bakuncin Nasarawa United ranar Laraba a kwantan wasan mako na biyu da ba su buga ba a gasar Firimiyar Nigeria wadda aka yi mako tara.

Ita ma Enyimba za ta fafata ne da Shoting Stars a kwantan wasan mako na biyu da ya kamata a ce sun yi a cikin watan Fabrairun shekarar nan.

Akwa United kuwa Elkanemi Warriors za ta ziyarta a kwantan wasan mako na uku, inda Wikki Tourists za ta fafata da Warri Wolves a kwantan wasan sati na shida.

Za a yi wasannin ne bayan da aka cire Akwa United da Warri Wolves da Nasara United daga gasar cin kofin zakarun Afirka, Enyimba ce kadai ke wakiltar Nigeria a gasar.

Akwa United ta yi wasanni takwas tana da maki 12 a mataki na takwas a kan teburi, Warri Wolves kuwa wasanni bakwai ta yi tana kuma mataki na 13 da maki 10.

Ita kuwa Enyimba wasanni biyar ta buga a gasar ta Firimiya tana kuma mataki na 18 da maki shida, yayin da Nasarawa United wadda ta yi fafatawa biyar tana matsayi na 20 da maki uku kacal.