Enyimba ta doke Shooting Stars da ci 2-0

Hakkin mallakar hoto NPFL Twitter
Image caption An buga wasanni tara a gasar ta Firimiyar Nigeria

Enyimba International ta samu nasara a kan Shooting Stars da ci 2-0 a kwantan wasan gasar Firimiyar Nigeria da suka fafata a ranar Laraba.

Abu Azeez ne ya fara ci wa Enyimba kwallon a minti na 33 da fara tamaula, kuma saura minti biyu ya rage a tashi daga wasan Osadiaye ya ci ta biyu.

Sauran sakamakon kwantan wasannin da aka yi Ifenyiubah ta samu nasara ne a kan Nasarawa United da ci daya mai ban haushi.

Elkanemi kuwa ta yi rashin nasara ne a hannun Akwa United da ci 3-1 a fafatawar da suka yi a jihar Katsina.

Wikki Tourist kuwa lallasa Warri Wolves ta yi da ci 4-0, kuma jumulla kwallaye 11 aka ci a kwantan wasanni hudu da aka yi a ranar ta Laraba.