Paraguay da Brazil sun tashi wasa 2-2

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Brazil za ta kara da Ecuador a wasanta na gaba a cikin watan Agusta

Paraguay ta buga 2-2 da Brazil a wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya da za a yi a 2018 a Rasha.

Paraguay ce ta fara cin kwallo ta hannun Dario Lezcano, sannan kuma Edgar Benitez ya kara ta biyu a ragar Brazil.

Brazil ta farke kwallon farko ta hannun Ricardo Oliveira, sannan ta zare ta biyu daf da za a tashi daga wasan ta hannun Daniel Alves.

Da wannan sakamakon da suka buga Brazil tana mataki na shida a kan teburi da maki tara, ita ma Paraguay maki tara ne da ita a matsayi na bakwai.

Uruguay ce kan saman teburi da maki 13 sai Ecuador ta biyu da maki 13 sannan Argentina da maki 11 a mataki na uku.

Brazil za ta ziyarci Ecuador a wasanta na gaba da za ta yi, inda Paraguay za ta karbi bakuncin Chile a ranar 29 ga watan Agustan shekarar nan.