Valencia ta raba gari da koci Neville

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption A cikin watan Disamba Valencia ta dauki Neville aiki

Kungiyar Valencia ta sallami kociyanta Gary Neville daga aiki, bayan da ya jagoranceta wasanni kasa da watanni hudu.

A cikin watan Disamba ne kungiyar ta bai wa Neville tsohon dan wasan Manchester United da Ingila aikin horar da ita.

A kuma cikin watan Fabrairu magoya bayan Valencia suka yi ta kiraye-kirayen a sallami kociyan, bayan da Barcelona ta doke Valencia da ci 7-0 a gasar Copa del Rey.

Valencia ta lashe wasanni uku daga cikin 16 da ta yi a League, kuma ya ci wasa 10 daga cikin karawa 28 da ya jagoranci kungiyar.