Sir Alex ya nemi a yi hakuri da Van Gaal

Image caption Van Gaal na shan suka kan halin da Man United ke ciki

Tsohon kociyan Manchester United Sir Alex Ferguson ya kare mai horar da 'yan wasan kungiyar na yanzu Louis van Gaal wanda ke shan caccaka daga magoya baya da kuma 'yan jarida saboda rashin kokarin kungiyar.

Sir Alex ya nemi da a ci gaba da hakuri da kociyan yana mai cewa nasara za ta dawo wa kungiyar.

Van Gaal ya kasa cin kofi ko da guda daya da kungiyar a tsawon shekara biyu da ya ke jan ragamar kungiyar, shi kuwa Ferguson wanda ya shafe shekara hudu kafin ya dauki kofinsa na farko da United din ya daukar mata kofuna 38 a shekara 22 daga nan.

Ferguson ya ce, ''a tarihin shekara 150 ba wani abu ba ne samun kai a yanayi na rashin katabus, domin abu ne da zai sake dawowa kuma idan zai komo zai dawo ne da karfin gaske.

Tsohon kociyan ya ce, ''idan dai kai mai goyon bayan Manchester United ne to sai ka zama mai hakuri, kuma wannan abu ne da magoya bayan suka nuna a shekarun baya, a zamanin Matt Busby da kuma lokacina.''

Ferguson wanda ya ce, ''abu ne mai matukar sauki a yi suka (na zaune gwanin kokawa)'' ya danganta matsalar da ta jefa kungiyar cikin halin katabus din da, raunin 'yan wasa da kuma yawan 'yan wasan da ta saya a lokacin bazara.

Van Gaal ya ci kofuna a Spain da Jamus da Holland, sanna kuma ya dauki kofin zakarun Turai da kungiyar Ajax a 1995.

Manchester United ba ta dauki wani kofi ba tun bayan da Sir Alex ya yi ritaya daga kungiyar a matsayin kociya , in ban da Community Shield a 2013, inda wanda ya gaje shi David Moyes ko kaka daya ma bai cika ba a kungiyar aka nada Van Gaal.

A yanzu dai United tana matsayi na shida ne a teburin Premier ko da yake maki daya ne kacal tsakaninta da ta hudu Manchester City.

A ranar 13 ga watan Afrilu ne za ta sake karawa da West Ham a wasan dab da na kusa da karshe na gasar kofin FA, amma ta sha kashi a hannun abokiyar hamayyarta Liverpool a gasar Europa.