An ci tarar Diego Costa Fam 20,000

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption An daga wa Diego Costa jan kati bayan da yaso ya ciji Gareth Barry

Dan wasan Chelsea na gaba, Diego Costa ba zai buga karin wasa guda daya ba sannan kuma an ci tarar sa Fam dubu 20, bayan amincewa da tuhumar nuna rashin da'a.

An dai hukunta dan wasan ne mai shekara 27, kan martanin da ya mayar lokacin da aka kore shi daga fili, a ranar 12 ga Maris, a wasansu da Everton na gasar FA.

Costa ya yi kacibis da Gareth Barry kuma ya so ya cije shi, duk kuwa da cewa Gareth ya ce babu abin da ya faru.

Tunda farko dai an dakatar da Costa daga buga wasanni biyu ne, amma yanzu an kara daya.

Yanzu haka, Costa ba zai buga wasan da kulob din nasa zai yi da Swansea ba, a ranar 9 ga Afrilu.