Kwallon kafar Najeriya na tangadi

Hakkin mallakar hoto Getty

Babu shakka Najeirya tana cikin manyan kasashen da suka yi nasara a kwallon kafa a nahiyar Afrika.

Kasar da ta yi nasarar lashe gasar zakarun Afrika sau uku, kuma kasa ta farko da ta lashe kyautar zinari a wasannin Olympics kazalika kasar da ta fi kowacce nasara lashe kofi a gasar 'yan kasa da shekaru 17 a wasannin Fifa, dole ma Najeriya ta amsa sunan ta.

Hakkin mallakar hoto Getty

Idan an hada da nasarar da kungiyar kwallon kafar kasa ta mata suka samu na kyaututtuka bakwai a gasar mata ta African Women championship, da ma wasu da suka samu a gasar 'yan kasa da shekaru 20, na matasan Afrika, to sai ka ga kasar ta yi fice sosai a kwallon kafa.

Amma kuma Najeriya ta soma komawa baya a shekaru biyu da suka gabata, kazalika rashin samun cancantar shiga gasar kofin kasashen Afrika ta shekarar 2017, ya nuna gazarwarsu.

Kungiyar ta Super Eagles baza su buga wasan karshe da Gabon ba, kamar dai yadda ta kasance masu a bara da Equtorial Guinea, bayan nasarar da suka samu a Afrika Ta Kudu a shekarar 2013.

Hakkin mallakar hoto Getty

Shekaru uku da suke wuce ne dai Stephen Keshi ya jagoranci tawagar 'yan kwallon suka yi nasara a gasar kofin kasashen Afrika, kazalika kuma ya a gasar cin kofin kasashen duniya da aka gudanar a Brazil a shekarar 2014.

Tun lokacin dai kamar da wasa Najeriya take kara yin kasa, har ta zamo abun kwatance ga al'umma, game da halin da wasannin kwallon kafa ta shiga a kasar.

Wasannin kwallon kafa a kasar da ta fi kowacce yawan al'umma a aAfrika, ta zamo lamari cike da tarzomar jagoranci, da cece-ku ce kan shugabanci, da rashin daidaito na siyasa da karanci kudin gudanar da ayyuka.

Gazawar Najeriya babu kwakkwarar dalili

Tsohon dan wasan kwallon kafa Segun Odegbami, wanda ke cikin manya a tawagar 'yan kwallo da suka samu nasarar gasar kofin kwallon kafa na kasashen a shekarar 1980, ya yadda da cewa ba za a samu nasarar a filin kwallo ba sai an samu daidaito a sashen tsare-tsare.

Rashin daidaito da ake samu wajen shugabancin tawagar, ya sa Hukumar kwallon kafa ta Najeriya, NFF ta sanya shugabanni shidda tun shekarar 2010- Shuaibu Amodu da Lars Lagerb├Ąck, da Austin Eguavoen, da Samson Siasia, da Stephen Keshi da kuma Sunday Oliseh.

Segun Odegbamu ya ce "Idan har ba a samu tushe mai inganci ba, to gine ko zai rushe har kasa."

Shugaban kungiyar kwallon kafa ta Najeriya, watau NFF Amaju Pinnick ya ce yana so ya yi hanzarin sauya alkiblar tawagar zuwa gasar kwallon kafa ta duniya ta shekarar 2018, tare kuma da tabbatar da cewa sashen shirye-shiryen bai samu matsalar rashin shugabancin kwarai ko rashin gudanar da sahihin aiki ba.

Tun bayan da ya soma jagorantar NFF a watan Satumbar shekara 2014, Pinnick ya nanata burinsa na sauya yadda ake gudanar da ayyukan kwallon kafa ta Najeriya.

Ya zuwa yanzu dai, hakarsa bata cimma ruwa ba.

Idan har ana so kwallon kafar Najeriya ta cigaba, to dole ne a samo wata hanya da zai bayar da muhalli mai ni'ima ga 'yan wasa da masu jagorantarsu, kazalika a baiwa sabbin masu tasowa kwarin gwiwa, domin a samu daidaito da kwanciyar hankali.