'Yan kwallon Amurka mata sun yi korafi kan albashi

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Sau uku kungiyar kwallon kafar mata ta Amuka na cin gasar kofin duniya
Manyan 'yan wasa biyar na tawagar ƙwallon ƙafar Amurka ta mata sun aike da ƙorafi suna kalubalantar hukumar ƙwallon ƙafar ƙasar da cewa ana nuna musu wariya kan abin da ake biyansu.

Alex Morgan da Carli Lloyd da Megan Rapinoe da Becky Sauerbrunn da kuma Hope Solo, sun ce ana biyansu ƙasa da rabin abin da ake biyan 'yan wasan kwallon ƙafa maza na ƙasar.

Ɗaya daga cikin 'yan wasa matan Hope Solo ta ce, "Tawagarmu ce Ƙungiyar wasa ta mata da ta fi kowacce a duniya, inda muka taƁa lashe gasar kofin duniya sau uku, amma sai gashi an fi fifita mazan wajen biyansu a kanmu.

Sai dai hukumar Ƙwallon ƙafar Amurkar ta ce bata ji daɗin abin da matan suka yi ba, ganin cewa ta yi aiki tuƙuru wajen gina wasan kwallon ƙafar mata da kuma ciyar da shi gaba.

A ranar Alhamis ne aka gabatar da ƙorafin ga hukumar daidaito kan biyan albashi.

Ɗaya daga cikin lauyoyin da suke kare matan Jeffrey Kessler, ya ce ƙungiyar wasan matan ta fi kawowa Amurka kuɗin shiga fiye da ta mazan, kuma lokaci ya yi da za a duba wannan lamari.