Arsenal ta ci Watford kwallaye 3-0

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Arsenal za ta ziyarci West Ham a wasan mako na 33 a gasar ta Premier

Arsenal ta samu nasara a kan Watford da ci 3-0 a gasar Premier wasan mako na 32 da suka fafata a Emirates ranar Asabar.

Sanchez ne ya fara ci wa Arsenal kwallon farko, kuma Iwobi ya ci ta biyu kafin a tafi hutun rabin lokaci.

Bayan da aka dawo ne daga hutun rabin lokaci Bellerin ya ci wa Arsenal kwallo ta uku, inda Walcott ya kuma ci ta hudu.

Arsenal ta doke Watford gida da waje kenan a gasar Premier bana, inda Watford ta fitar da Arsenal daga gasar FA, kofin da take rike da shi.

West Ham ce za ta karbi bakuncin Arsenal a wasan mako na 33, yayin da Watford za ta karbi bakuncin Everton.

Ga yadda wasanin na Premier na Asabar din suka kasance Aston Villa 0 - 4 Chelsea ; West Ham United 2 - 2 Crystal Palace Bournemouth 0 - 4 Manchester City ; Norwich City 3 - 2 Newcastle United ; Stoke City 2 - 2 Swansea City ; Arsenal 4 - 0 Watford Sunderland 0 - 0 West Bromwich ; Liverpool 1 - 1 Tottenham Hotspur