EURO2016: Watakila Bastian ba zai yi wasa ba

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Schweinsteiger ya ji rauni ne a lokacin wasan sada zumunta da Ingila

Watakila kyaftin din Jamus, Bastian Schweinsteiger, ba zai buga gasar cin kofin nahiyar Turai ba, sakamakon raunin da ya ji.

Kociyan Manchester United, Louis van Gaal, ne ya bayar da wannan sanarwar, inda ya kara da cewar dan kwallon zai iya yin jinya mai tsawo.

Schweinsteiger ya ji rauni ne a lokacin da yake yi wa Jamus wasan sada zumunta a karawar da suka yi da Ingila.

Kociyan ya kuma ce mai tsaron bayansa Luke Shaw, zai dawo yin atisaye a mako mai zuwa.

Kasar Faransa ce za ta karbi bakuncin gasar cin kofin nahiyar Turai da za a yi a bana.