An ci kwallaye 182 a gasar Firimiyar Nigeria

Hakkin mallakar hoto NPFL Twitter
Image caption An ci kwallaye 182 a raga a gasar Firimiyar Nigeria

An zura kwallaye 182 a gasar Firimiyar Nigeria, bayan da aka kammala wasannin mako na tara a gasar.

Dan wasan Lobi Okpotu shi ne ke gaba a yawan cin kwallaye a gasar, inda ya zura guda shida a raga.

Wadanda suka ci kwallaye biyar-biyar kuwa sun hada da Jimoh na 3SC da Egbuchulam na Rangers da Mustapha na kungiyar El-Kanemi.

'Yan wasan da suka ci hudu-hudu a raga sun hada da Gata na Tornadoes da 'yan wasan Pillars Ali da Aggreh da Eduwo na Lobi da kuma Obaje na Wikki Tourist.